Ban Damu Da Binciken Da Gwamnatin Kano Ke Yi Ba – Ganduje

Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ganduje, ya bayyana cewa babu wata damuwa kan binciken da gwamnatin jihar Kano ke gudanarwa kan zargin cewar an ɗauki kuɗin jihar aka saka su a tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port.

Martanin ya fito ne ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai na jihar, kuma tsohon shugaban ma’aikatan Ganduje, Muhammad Garba, inda ya bayyana cewa, wannan maganar tana gaban kotu, don haka bai san irin binciken da ake nufi ba.

Ya ce lokacin da ya tuntuɓi tsohon gwamnan, ya ce babu abin da ke damunsa, domin irin waɗannan binciken ba sabon abu ba ne.”

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar Karɓar korafe-ƙorafe da Hana Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗe fiye da naira biliyan huɗu da ake zargin tsohuwar gwamnatin da yi , kamar yadda shugaban hukumar, Saidu Yahaya, ya tabbatar da cewa binciken ya biyo bayan ƙorafi da aka shigar mu su.

Haka zalika a ranar Laraba kamfanin Dala Inland Dry Port (DIDP) ya musanta rahotannin da ke cewa iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, suna da hannun jari ko wani nau’in mallaka a kamfanin.

A cikin wata sanarwa da Sakatare na Kamfanin, Barista Adamu Aliyu Sanda, ya fitar ranar Laraba, kamfanin ya bayyana rahotannin a matsayin “karya da rudani mai cike da siyasa,” yana mai cewa babu wani daga cikin iyalan Ganduje ko Gwamnatin Jihar Kano da yake da hannu a cikin mallaka ko shugabancin kamfanin.

“Zarge-zargen da ke cewa iyalan Ganduje suna cikin masu hannun jari ko shugabanni a Dala Inland Dry Port karya ce gaba ɗaya,” in ji Sanda. “Binciken da aka tabbatar daga Hukumar Rajistar Kamfanoni (CAC) da kuma takardun hukumar ya nuna babu wani daga cikin iyalan Ganduje da ya taɓa kasancewa ɗan hannun jari, darakta ko mai sanya hannu a harkokin kamfanin.”

Barista Sanda ya bayyana cewa, asalin mallakar kamfanin na hannun wani ɗan kasuwa mai suna Ahmad Rabi’u, kafin City Green Enterprises (CGE) ta sayi kaso 80 cikin 100 na hannun jarin kamfanin, ta bar Rabi’u da kaso 20 cikin 100.

Wannan cinikayya, a cewar sa, ta kasance karkashin tsarin doka kuma an tabbatar da ita a Hukumar CAC ba tare da wani hannun iyalan Ganduje ko gwamnatin Kano ba.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda