Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku.
Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, Bright Edafe, ya ce ’yan sanda sun samu ƙorafi a kan faston bisa zargin lalata, fyade da cin zarafi.
Ya ce a ranar 17 ga watan Nuwamba, an kama wanda ake zargi a harabar cocinsa.
- Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi
- Yan Sandan Jihar Neja Sun Bugi Kirjin Sai Sun Ceto Daliban Da Aka Sace
Edafe ya ce bincike ya nuna faston ya yi amfani da mu’ujiza ta karya wajen jawo mambobin cocin masu rangwamen gata zuwa ofishin cocinsa, yana tilasta musu su yi imani cewa idan bai yi jima’i da su ba, ba za su sami ’yanci ba.
Ya ƙara da cewa bincike ya tabbatar da cewa faston ya yi lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne, inda ya ce wacce ake zargin ya yi wa fyadeb ta ƙarshe shekararta 17.
Edafe ya ce wanda ake zargi yana tsare a hannun ’yan sanda yayin da bincike ke ci gaba da gudana.