An Kama Mai Kai Wa Turji Makamai 

Rundunar Sojin Operation Fansar Yamma, sun kama wata mata mai shekara 25 a Jihar Zamfara da ke kai wa ƙasurgunin ɗan ta’adda Bello Turji Makamai a jihar Zamfara. 

Dakarun rundunar sojin sun kama matar ne ɗauke da alburusai 764 da bindigogi guda shida.

Wannan bayani na ƙunshe a cikin wata sanarwa da kakakin Operation Fansar Yamma, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar.

Ya ce, an kama matar tare da wani abokin tafiyarta ne a ranar Asabar 28 ga watan Disamba, a yankin Badarawa, a Ƙaramar Hukumar Shinkafi jihar Zamfara.

Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya ce sun samu wannan nasara ne bayan samun rahoton sirri kan safarar makamai a yankin.

 

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa