Abba Ya Taya Babandede Alhinin Rashin Mahaifiyarsa

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya miƙa saƙon ta’aziyya ga tsohon Shugaban Hukumar shigi da fici ta Najeriya kuma mamallakin tashoshin talabijin da radio na MUHASA Muhammad Babandede bisa rashin mahaifiyar sa da yayi a ranar Alhamis.

Muhmmad Babandede ya rasa mahaifiyarsa Hajiya Hajara mai shekaru 90 a ranar Alhamis bayan rashin lafiya da tayi a asibitin Malam Aminu Kano.

Cikin saƙon da ya fitar ta bakin mai magana da yawun sa Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamna Abba ya bayyana Marigayiya Hajiya Hajara a matsayin mace mai tsoron Allah da kiyaye iyakokin addinin musulunci.

Gwamna Abba ya kuma  jinjinawa tsohon Shugaban Hukumar na shigi da fici Muhammad Babandede bisa irin namijin Kokorin da yayi a lokacin da yake shugabancin hukumar.

A ƙarshe yayi addu’ar Allah ya jikanta da rahama, ya kuma bashi ikon jure wannan babban rashin.

 

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya