An Sa Dokar Hana Fita A Mazabar Sanata Natasha

Rahotanni daga karamar hukumar Okehi a jihar Kogi, mazabar Sanata Natasha Akpoti, na cewa Shugaban karamar Hukumar Amoka Monday, ya sanya dokar hana fita, saboda matsalar tsaro biyo bayan hana tarukan siyasa da na jama’a ba bisa ka’ida ba.

A cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa sanya dokar hana fita ya zama wajibi domin wanzar da zaman lafiya da kuma bin umarnin gwamnatin jihar Kogi da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, duk wanda aka samu yana taro ko kuma hada mutane ba tare da izini daga hukumomin da abin ya shafa ba za a kama shi kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Wanna na kunshe a cikin wani rahoto da kafar yada labarai DCL Hausa ta wallafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *