An Yi Jana’izar Tsohon Sakataren Gwamnatin Borno Alh. Muh’d Kagu 

Daga: Mohammed Garundole

Allah ya yi wa tsohon Sakataten gwamnatin jihar Borno Marigayi Alhaji Mohammed Kagu Alibe rasuwa da safiyar yau Asabar a asibitin koyarwar Jami’ar Maiduguri. 

An gabatar da Sallar Janaizar Alhaji Mohammed Kagu Alibe a gidansa dake old GRA, Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Janaizar ta samu halartar Gwamnan jihar Borno Farfesa Baba Gana Umara Zulum da mukarrabansa dakuma tsohon Shugaban Hukumar Shigi da fice ta kasa, kuma Shugaban gidan Radio da talabijin na MUHASA Alhaji Mohammed Babandede OCM OFR.

Alhaji Mohammed Kagu Alibe ya rasu yana da shekaru 81, ya bar mata ɗaya Hajiya Aisa k Alibe, da ‘ya’ya biyu biyu da kuma jikoki biyu.

Ya bar yayyu da ƙanne ‘yan uwa da dama.

Post masu alaƙa

Yar Najeriya ta kammala jami’ar Burtaniya da daraja ta daya (1st Class) a ilimin kimiyar samar da manhajar kasuwancin zamani.

Gwamnati ta buƙaci jama’a su guji taɓa kumfar da ta ɓulla a hanyar Kaduna-Abuja

A riƙa yi wa masu shirin aure gwajin miyagun ƙwayoyi :- Buba Marwa