An yi musayar wuta tsakanin ’yan sanda da gungun wasu ’yan fashin motoci da suke yi ƙoƙarin sace wasu motoci a kan titi a Abuja.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja , Miller G. Ɗantawaye, wanda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da dare, a kusa da Gadar Efab, yayin da jami’an ke gudanar da aikin bincike na yau da kullum.
Ya ce ’yan fashin su hudu suna isowa wurin da ’yan sandan daga shiyyar Galadimawa suke, sai suka buɗe wa jami’an wuta, suna ƙoƙarin sace wasu motoci biyu: Hyundai Elantra (2014) da kuma Lexus Jeep (2008).
A cewarsa, jami’an sun mayar da martani cikin gaggawa inda suka di ƙarfin ɓata-garin. Haka ya tilasta wa masu laifin barin motocin sannan suka gudu daga wurin.
- Jiragen soji sun yi raga-raga da rumbun makaman Boko Haram a Borno
- Sojoji sun ceto mutane 3 daga cikin 5 da aka sace a Kano
Kwamishinan ’yan sanda ya ce an fara gudanar da bincike domin ganowa, bin diddigi da kuma cafke waɗanda ake zargin.
CP Dantawaye, ya jaddada kudirin rundunar wajen hana aikata laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Abuja.
Ya kuma bukaci jama’a su ci gaba da zama masu bin doka da lura da tsaro, tare da gaggauta kai rahoton duk wani mutum ko aiki da ake zargin ba daidai ba zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa, ko ta layin wayoyin gaggawa na rundunar: 08032003913, 08028940883
