Home » Ana Zargin Alaƙa Ta yi Tsami Tsakanin Abba Da Kwankwaso

Ana Zargin Alaƙa Ta yi Tsami Tsakanin Abba Da Kwankwaso

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Lamari na ƙara rincaɓewa a jam’iyya mai mulki a Kano NNPP, inda wasu majiyoyi suka tabbatar da cewa gwaman Abba ya daina ɗaga kiran mai gidansa Sanata Rabi’u Kwankwaso.

Wannan dambarwa dai na kara karfi tun bayan ɓullar wata sabuwar ƙungiya mai suna “Abba tsaya da kafar ka”, da ke rajin gwamnan ya yi ta ware irin na siyasa da mai gidan na sa don ganin ya gina tasa tafiyar.

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa ƙoƙarin raba kan gwamnan da mai gidansa an ɗakko shine ta hanyoyi daban daban.

Ana zargin Sakataren gwamnatin Kano Dokta Baffa Bichi na daga cikin na gaba-gaba wurinn jagorantar yin bore ga jagoran.

Wasu majiyoyi sun tabbatarwa wa da jaridar cewa zuwa yanzu gwamnan baya amsa kiran wayar mai gidan na sa Sanata Kwankwaso.

“Abba ba ya so ya watsa wa mai gidan na sa kasa a ido, amma tabbas yana da muradun samun iko a matsayin sa na gwamna.
“Kaso 90 na kwamishinonin gwamnatin Kano, Kwankwaso ne ya naɗa su, amma Abba yana aiki dasu ne don nuna girmamawa.” A cewar majiyar.

Majiyar ta ƙara da cewa haƙurin gwamnan ya zo karshe musamman yanda jagoran ya shiga al’amuran zaɓen kananan hukumomi a jihar.

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa matsalar ta samo asali ne bayan da Kwankwaso ya naɗa kantomomi 44 a faɗin jihar ba tare da jin ta bakin gwamna Abba ba.

Amma a ranar 19 ga watan Satumba, gwamnan ya rufe ido ya tsige kantomomin, sati guda bayan da majalisar dokokin jihar ta ƙara wa’adin su da watanni biyu.

Alaƙar ta ƙara tsami bayan da ake zargin Kwankwaso ya zaɓi sabbin ciyamomi da Kansiloli ba tare da shawartar gwamnan ba.

Majiyar ta ce, in ban da taron murnar zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso da aka yi a ranar 21 ga watan Oktoba, gwamnan da sanata Kwankwaso sun ɗauki lokaci ba sa magana.

Bayan da lamari ya ƙara rincaɓewa, majiyoyi sun tabbatarwa jaridar cewa gwamnan ya kauracewa taruka da dama da Kwankwaso ya kira, ba tare da wani uzuri ba.

Bugu da ƙari Kwankwaso ya sake bin gwamna Abba Abuja, to sai dai haduwar su bata yiyu ba.

Bayan duk ƙoƙarin Kwankwaso na ganin ya gana da Abba ta ci tura, duk da bi da yayi ta hannun sakataren sa.

Ana ganin wannan alamu ne dake nuna cewar Gwamnan ya fara bin huɗubar da ake na ya tsaya da kafar sa, tun bayan da jigo a jam’iyyar kuma ɗan Majalisa mai wakilta Dala a Majalisar ƙasa Ali Madakin Gini ya fice daga jam’iyyar tare da Hon Alhassan Rurum, an hangi Madakin gini cikin wani faifan bidiyo yana kira da gwamnan da ya tsaya da ƙafar sa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?