An Ceto Yaran Arewa A Onitsha Da Aka Sato Da Sunan Marayu
Dubun wasu ɓarayin yara ta cika bayan an kama su da satan yara daga jihar Taraba dake Arewa Maso Gabashin Najeriya zuwa kudu maso gashin ƙasar.
Dubun wasu ɓarayin yara ta cika bayan an kama su da satan yara daga jihar Taraba dake Arewa Maso Gabashin Najeriya zuwa kudu maso gashin ƙasar.
Rahotanni daga jihar Filato na cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos sun kai 52.
Kotun Ƙoli ta soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta yanke wanda ya amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP na ƙasa.
Dubban Mutane daga sassan Najeriya ne suka Halarci Jana’izar Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi wanda Allah ya yi wa rasuwa a daren Alhamis.
Tsohon mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa.
Tsohon shugaban Hukumar Bautar Kasa A Najeriya Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta daga hannun ‘yan ta’adda masu satar mutane bayan shafe kwana 56 a sace.
Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu ƙaramin ƙarfi.
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar karkashin jagorancin Janar Abdurrahmane Tchiane ta bayyana janye dakarunta daga rundunar Hadin Gwiwa mai yaki da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.
Rahotanni daga karamar hukumar Okehi a jihar Kogi, mazabar Sanata Natasha Akpoti, na cewa Shugaban karamar Hukumar Amoka Monday, ya sanya dokar hana fita, saboda matsalar tsaro biyo bayan hana tarukan siyasa da na jama’a ba bisa ka’ida ba.
Sanata Natasha Akpoti wadda a kwanan nan Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar na tsawon watanni shida, ta ce “babu gudu babu ja da baya dangane da gangamin gaisuwar Sallah” da ta shirya yi a mazaɓarta.