Tsohon shugaban Hukumar Bautar Kasa A Najeriya Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta daga hannun ‘yan ta’adda masu satar mutane bayan shafe kwana 56 a sace.
An sace Janar Tsiga ne ranar 5 ga watan Fabrairu 2025, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina.
‘Yan ta’addar a lokacin da suka sace janar Tsiga ne tare da wasu mutane tara a lokacin da suka kai harin.
Rahotanni su bayyana cewa duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, ’yan bindigar sun ci gaba da tsare shi na tsawon makonni.
Wasu majiyoyin sun ce Naira miliyan 60 aka biya, amma wasu masu tushe sun ce an biya sama da haka.
Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa bayan maharan sun karɓi kuɗin, sai suka yi shiru har na tsawon mako guda, kafin daga bisani su kira iyalansa a ranar 11 ga watan Maris, inda suka ba shi ya yi magana da su.
Daga baya, sun sake neman ƙarin kuɗi, amma iyalan nasa ba su ƙara musu ba.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa yanzu haka yana Jihar Zamfara, wanda daga nan za a kai shi Abuja.
Wani jami’in soja ya tabbatar da sakinsa, inda ya ce yana cikin ƙoshin lafiya.