Jamhuriyar Nijar Ta Fice Daga Kawancen Yakar ‘Yan Ta’addan Boko Haram

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar karkashin jagorancin Janar Abdurrahmane Tchiane ta bayyana janye dakarunta daga rundunar Hadin Gwiwa mai yaki da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.
Gwamnatin ta ce ta  janye dakarun nata ne domin mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron bututun mai na ƙasar da ke fuskantar hare-haren ƴan bindiga.
Wannan mataki na gwamnatin jamhuriyar Nijar ya zo wa mutane da dama da fuskoki daban daban inda wasu ke ganin an yi dai dai, wasu kuma ke ganin akasin haka.
A baya bayan nan ne dai aka tabbatar wa Janar Abdurrahmane Tchiane wa’adin mulki na shekara biyar, inda ake sa ran kafin wannan lokacin, zai inganta rayuwar kasar da ‘ya’yanta.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.