Ba mu da shirin sauke Sarki Sanusi II — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga kan mulki bayan sauya sheƙar gwamnan daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Aminiya kan lamarin ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa a ranar Juma’a.

Sanusi Bature ya ce “babu wani shiri na sauya Sarkin Kano Sanusi II, kwata-kwata” a halin da ake ciki.

Ya ƙara da cewa “an naɗa sarkin ne bayan an soke tsohuwar dokar masarautu, kuma babu wani shiri da gwamnati ke yi na yin wani ƙarin gyaran.

“An naɗa Sarkin Sanusi bisa doka bayan soke tsohuwar dokar, kuma sauya sheƙar gwamnati zuwa APC ba zai canza komai ba.

“Sarki Sanusi II har yanzu shi ne Sarkin Kano. Babu wani yunƙuri, babu wata niyya ta maye gurbinsa, ” a cewarsa.

Post masu alaƙa

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi