Gwamnatin tarayya na shirin samar da motoci masu amfani da iskar gas
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamiti na musamman da zai samar da motoci masu amfani da Iskar Gas da kuma tashoshi na sayar da isakar gas domin karfafa shirin fara amfani da motoci masu amfani da shi a fadin kasar nan.