Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano Ya Amince da Naɗa Karin Mataimaka 94
A ƙoƙarinsa na tabbatar al’ummar Kano sun samu labarai game da ayyukan gwamnatinsa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin karin masu taimaka masa na musamman a matsayin masu ɗaukar rahoto a ma’aikatu da hukumomi daban-daban na jihar Kano.