ADC Ta Rusa Shugabancin Jam’iyyar a Kano, Ta Kafa Kwamitin Riƙo.

adc

Jam’iyyar ADC ta rusa shugabancinta na Jihar Kano tare da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da zai jagoranci harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaɓen shugabanni.
Mataimakiyar Shugabar ADC ta ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Najaatu Muhammad, ce ta sanar da hakan a ranar Litinin yayin taron manema labarai da aka gudanar a Kano.
A cewarta, an naɗa Alhaji Umar Bala a matsayin shugaban kwamitin riƙon ƙwaryar da zai jagoranci jam’iyyar na ɗan lokaci.
Hajiya Naja’atu ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kuma ba wai don fifita wani ɓangare ba ne.
Ta ce manufar ita ce dawo da daidaito, tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin jam’iyyar, tare da cike giɓin shugabanci da ya taso a jihar.
Ta kuma yaba wa mambobin jam’iyyar ADC a Kano bisa gudummawar da suka bayar wajen bunƙasa jam’iyyar, tana mai jaddada cewa shugabancin ƙasa na ADC na matuƙar girmama jajircewarsu da sadaukarwar da suka nuna.

Post masu alaƙa

Barau Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Arewa A APC

Sanata ya bar APC a jajibirin zaɓen fidda gwani a Kebbi 

Yusuf Buhari ya lashe zaɓen takarar majalisar tarayya a APC