An Kama Ɗan Ƙasar Angola Kan Safarar Miyagun Kwayoyi A Najeriya
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta cafke wani ɗan kasuwa ɗan asalin ƙasar Angola, Mbala Dajou Abuba, mai shekaru 42, a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, yayin da yake ƙoƙarin safarar hodar iblis zuwa ƙasar Turkiyya.