EFCC Ta Tabbatar Da Yin Kame A Wani Otal A Neja

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta ce ita ta kai samame otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Minna, Babban Birnin Jihar Neja.

A yayin farmakin, an kama aƙalla baƙi 10 da ake zargi da aikata damfara a Intanet, wanda aka tafi da su Kaduna.

Wani ma’aikacin otal ɗin da ya nemi a sakaya sunansa, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ’yan bindiga ne suka yi basaja a kayan EFCC, sula sace baƙi 10 a ranar 27 ga watan Fabrairu.

“Ba ’yan bindiga ba ne. Jami’an EFCC ne suka zo suka kama wasu ‘yan damfara suka tafi da su Kaduna,” in ji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya kuma yi watsi da wannan jita-jitar.

Ya shawarci ’yan jarida su tuntuɓi EFCC domin tabbatar da sahihancin lamarin.

 

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya