DSS ta kama wani matashi da ake zargi da safarar makamai a Kano
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama wani mutum mai shekara 30 da haihuwa, Muhammad Abubakar, bisa zargin safarar makamai a Jihar Kano. DSS ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ƙaramar hukumar Gezawa bayan samun bayanan sirri, yayin da yake kokarin kai bututun makamin roka guda huɗu (RPG), bindigogi kirar […]