Labarai

Kwamandan NSCDC ya gana da mahukuntan tashar tsandauri ta Dala Dry Port Kan inganta tsaro.

Kwamandan hukumar tsaron civil defense reshen jihar Kano, Muhammad Hassan Agalama, IION, ya gana da mahukuntan tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port a Kano, inda suka tattauna hanyoyin ƙara inganta tsaro da kare tashar daga duk wata barazana. Ganawar, wadda aka gudanar a ofishin kwamandan a cikin makon nan, ta mayar da hankali ne kan muhimmancin […]

Read more

ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28

Jam’iyyar ADC ta fitar da sunayen ’yan takararta na gwamna da mataimakin gwamna a jihohi 28 domin tunkarar zaɓen 2027. Jerin ya ƙunshi wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP, Isa Ashiru, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Sauran sun haɗa da tsohon ɗan takarar gwamnan Delta, Great Ogboru, […]

Read more

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Allah Ya yi wa Mai martaba Sarkin Gumel, Alhaji Dakta Ahmed Muhammad Sani II, CON, rasuwa. Rasuwar Sarkin ta jefa al’ummar Masarautar Gumel da sauran al’ummar Jihar Jigawa cikin jimami da alhini, musamman kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan sarakunan gargajiya da suka daɗe suna taka muhimmiyar rawa wajen jagoranci da zaman lafiyar al’umma. Sarkin ya […]

Read more

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

Rahotanni daga yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da ke Jihar Katsina sun ce jami’an tsaro sun kashe wasu manyan kwamandojin ’yan bindiga biyu a wani artabu da suka yi da ’yan ta’addan da ke ƙarƙashin jagorancin wani da ake kira Kachalla Fulani. Majiyoyi sun ce artabun ya biyo bayan wani harin kwanton ɓauna da ’yan bindigar […]

Read more