Labarai

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta kafa kwamitin da zai nemo hanyoyin da jami’anta za su mallaki gidaje.

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ƙirƙiro wani kwamiti da zai  fito da hanyoyin da kowanne jami’in ɗan sanda zai mallaki muhalli ba tare da yasha wahala ba. Muƙaddashin babban sufeton ƴan sanda Najeriya, DIG Sulaiman Muhammed Abdul, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da dakarun ƴan sandan jihar Kano, a madadin shugaban ƴan […]

Read more

Gwamnatin Katsina ta haramta sana’ar POS da cajin waya

Gwamnatin Katsina ta haramta gudanar da sana’ar cirar kuɗi ta PoS da cajin waya da kuma haya da babur a yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da Musawa ta Jihar nan take. Sabuwar dokar zartarwar da Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu ta kuma haramta sayarwa da jigilar man fetur a cikin jarkoki a fadin jihar nan […]

Read more

Kada ku damu kan batun kafa ’yan sandan jihohi —Sufeto-Janar

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya tabbatar wa jami’ai da ma’aikatan rundunar cewa shirin kafa ’yan sandan jihohi ba zai kawo ƙarshen rundunar ’yan sanda ta ƙasa ba.   Disu ya bayyana haka ne a ziyararsa ta farko a hukumance ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa a ranar Litinin. Ya ce babu dalilin […]

Read more

Kotu ta umurci INEC ta soke rijistar jam’iyyar ADC

Wata babbar Kotun Tarayyar Najeriya ta umurci hukumar zaɓen ƙasar INEC ta soke rajistar jam’iyyar adawa ta ADC da wasu jam’iyyu huɗu. Kotun da ke Abuja ta ce jam’iyyun sun gaza cika sharuɗan da kundin tsarin mulkin kafa jam’iyyun siyasa. Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin, inda ya ce jam’iyyun ba su samu […]

Read more

Ɗan Kwankwaso ya zama ɗan takarar Mataimakin Gwamnan Kano a NDC

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zaɓi Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna a Zaɓen 2027. Mustapha Kwankwaso, wanda tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni ne a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, ya yi murabus daga muƙaminsa, inda ya koma tafiyar […]

Read more

Yan bindiga sun lafta wa manoma sabbin haraji a Sakkwato

Mazauna akalla ƙauyuka 26 a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato sun fara tara kuɗi domin biyan sabon harajin da ‘yan bindiga suka ƙaƙaba musu kafin noma gonakinsu a daminar bana. Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa ’yan ta’addan sun yi barazanar yin garkuwa ko halaka duk wanda suka gani yana aikin gona […]

Read more