Wata babbar Kotun Tarayyar Najeriya ta umurci hukumar zaɓen ƙasar INEC ta soke rajistar jam’iyyar adawa ta ADC da wasu jam’iyyu huɗu.
Kotun da ke Abuja ta ce jam’iyyun sun gaza cika sharuɗan da kundin tsarin mulkin kafa jam’iyyun siyasa.
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin, inda ya ce jam’iyyun ba su samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da doka ta tanada a zaɓukan da suka gabata ba.
Jam’iyyun da hukuncin ya shafa su ne ADC, Accord, AA, APP da ZLP. Ya bayyana cewa jam’iyyun taka sashe na 225 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kotun ta kuma umarci INEC da kada ta bari jam’iyyun su shiga zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban Zaɓen 2027, matuƙar ba su cika sharuɗan da doka ta tanada ba.
Wata ƙungiyar tsofaffin ƴan majalisa ta shigar, inda ta yi zargin cewa jam’iyyun sun kasa cika ƙa’idojin da suka shafi samun goyon baya da kuma sakamakon zaɓe.
Sai dai jam’iyyar ADC ta fitar da sanarwar cewa za ta shiga zaɓen 2027 kuma tana kira ga mabiyanta da su yi watsi da hukuncin.