Labarai

Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno

Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya. Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:40 na rana a bayan tashar motar Banki […]

Read more

Senata Ndume ya buƙaci Tinubu ya janye sunayen jakadu

Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Ali Ndume, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye jerin sunayen jakadun da ke gaban majalisar a halin yanzu, bisa zargin cewa an saba wa ƙa’idar tsarin tarayya da kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada. A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne majalisar […]

Read more

Kungiyar Malamai Ta NUT Ta Karrama Malam Umar Namadi Da Lambar Yabo Ta “Gwamna Mafi Ƙwazo

Kungiyar Malamai ta Najeriya, NUT, ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da lambar yabo ta “Gwamna Mafi Ƙwazo a Arewacin Najeriya” a bangaren ilimi, saboda manyan gyare-gyaren da gwamnati ta aiwatar a fannin. Tawagar NUT daga jihohi 19 na Arewa, ƙarƙashin jagorancin Comrade Muhammad Hambali, ta kai ziyara Fadar Gwamnatin jihar da ke […]

Read more