Rundunar ƴansandan Najeriya tare da haɗin gwiwar cibiyar yaƙi da laifukan intanet ta ƙasa (NPF–NCCC) ta bayyana cewa ta bankaɗo wata babbar ƙungiyar masu satar katin waya ta intanet da ta haddasa asarar kuɗi da ta haura naira biliyan 7.7.
’Yan sandan sun ce ƙungiyar na karkatar da katin waya da bayanan intanet na wani kamfanin sadarwa ta haramtacciyar hanya.
Rundunar ce ta sanar da hakan a shafinta na X.
Hakan ya biyo bayan ƙorafin da wani kamfanin sadarwa a Najeriya ya shigar, inda ya lura da wasu ayyuka na zamba da ba a amince da su ba a tsarin biyan kuɗaɗe da lissafin kamfanin.
Binciken ’yansanda ya nuna cewa an sace bayanan wasu ma’aikatan kamfanin ne lamarin da ya bai wa masu laifin damar shiga muhimman tsarin kamfanin ba tare da izini ba.
Bayan makonni na shiri da bincike, ’yansanda sun gudanar da samamen kama mutane a jihohin Kano da Katsina a watan Oktoban 2025, tare da wani kama ƙarin wasu da ake zargi a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A yayin wannan aiki, an kama mutum shida da ake zargi.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da gidaje biyu a Kano, ƙananan kantuna biyu, shagunan sayar da wayoyi da kwamfutoci da ke ɗauke da sama da kwamfutoci 400 da wayoyi 1,000.
Haka kuma, an gano kuɗaɗe masu yawa a asusun bankin waɗanda ake zargin wanda ƴansanda suka kyautata zaton cewa kuɗaɗe an same su ne ta hanyar aikata laifin.
’Yan sanda sun ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.