Babban Labari

‘Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce dakarun juyin juya halin Iran sun buɗe wa wani jirgin dako wuta a mashigar Hormuz. Lamarin ya faru ne kimanin mil 23 daga arewa maso gabashin Oman. UKMTO ta ce ma’aikatan jirgin sun samu kuɓuta daga harin. A wani labarin na daban, wasu jiragen […]

Read more

Ƙungiyoyin PDP 293 sun koma APC a Yobe

A wani gagarumin sauyin siyasa a Jihar Yobe, ƙungiyoyi 293 na Jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a Ƙaramar Hukumar Potiskum.   Sauyin sheƙar wanda shi ne mafi girma a yankin a ’yan kwanakin nan ya samu jagorancin Shugaban PDP na Ƙaramar Hukumar Potiskum, Alhaji Audu Hamisu, wanda aka fi sani da Soja Boy. Masu […]

Read more

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta Jihar Yobe ta bayyana neman wani fursuna ruwa a jallo bayan ya tsere daga wurin da aka yi hatsarin mota sa’ilin da ake jigilar fursunoni daga Potiskum zuwa Damaturu. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Adamu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da […]

Read more

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto

Wani rahoto da hukumar ƙididdigar jihar Sokoto ta fitar ya nuna cewa yanzu haka girman talaucin ya faɗo ƙasa warwas daga kaso 91 zuwa 41. Rahoton ya alƙanta cigaban da aka samu da irin ƙokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen inganta rayuwar al’ummar karkara, inda a shekarar 2026 gwamnatin ta ware kaso 70 na […]

Read more

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Wani mai buga bulo ya riga mu gidan gaskiya bayan da wani da ake zargin ɗan daba ne, wanda aka fi sani da Aboy, ya daɓa masa wuƙa kan Naira 200 a wata gidan bulo da ke yankin Ota a Jihar Ogun. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar 1 ga watan Afrilu a masana’antar […]

Read more

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a yankin Ikot Ekpene na jihar Akwa Ibom sun yi watsi da shirin baiwa ɗan takara tikitin kai tsaye domin kujerar majalisar dokokin jihar mai wakiltar Ikot Ekpene/Obot Akara, gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, inda suka bayyana hakan a matsayin saɓawa ka’idojin dimokuraɗiyya. An bayyana matsayar ne […]

Read more