Babban Labari

Harin Iran ya jikkata sojojin Amurka 12 a Saudiyya

Rahotanni sun ce wani harin makami mai linzami daga Iran ya jikkata sojojin Amurka 12 a wani sansanin soji da ke Saudiyya. Jami’ai sun shaida wa abokiyar hulɗar BBC, wato CBS, cewa wasu daga cikin sojojin sun samu munanan raunuka a sansanin jiragen sama na Yarima Sultan. Harin ya kuma lalata wasu jiragen sojin saman […]

Read more

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Murabus

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi murabus daga muƙaminsa. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar Kwankwasiyya ta fitar, wadda kakakinta Dr Habibu Sale Mohammed ya fitar da yammacin ranar Juma’a. Ya ce mataimakin gwamnan ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano da tabbatar […]

Read more

Mahaifiyar Nasir El-Rufai ta rasu

Mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai mai suna Hajiya Umma El-rufai ta rasu. Ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai ne ya sanar da rasuwar a ranar Juma’a, inda ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ina sanar da al’umma cewa Allah ya yi wa kakata, Hajiya Umma El-Rufai […]

Read more

Najeriya ta doke Iran da ci 2 a wasan sada zumunta

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, ta doke ƙasar Iran da ci 2 da 1 da wasan sada zumunta da suka buga a ranar Juma’a. Ƙasashen biyu sun kara da juna a filin wasa na Mardan Sport Complex da ke yankin Antalya na ƙasar Turkiyya. Ɗan wasan gaban Super Eagles, Moses Simon ne ya […]

Read more

Kotu ta ɗage sauraron buƙatar bada belin El-Rufai

Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga Maris, 2026. An ɗauki wannan matakin ne bayan zaman kotun na ranar Talata, inda ɓangaren masu ƙara da masu kare kai suka gabatar da hujjoji. A zaman kotun, lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan ya buƙaci […]

Read more

EFCC ta ƙwace gidajen Malami a Abuja

Jami’an Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa sun yi wa gidajen tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami ƙawanya a wani yunkuri na ƙwace muhallin tsohon Babban Lauyan na Najeriya. Tun dai a ranar Litinin da ta gabata ce jami’an EFCCn suka ka ziyarci wasu gidajen tsohon ministan da ke Maitama […]

Read more