Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da harin da aka kai Maiduguri
Kungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF) ta yi Allah-wadai da mummunan harin ƙunar-baƙin-wake da ya auku a yammacin jiya na Litinin a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Aminiya ta ruwaito yadda aka samu tashin bama-bamai kashi uku a kusan lokaci guda a Asibitin Koyarwa na Maiduguri da babbar kasuwar nan ta Monday Market da kuma yankin Gidan […]