Babban Labari

An karrama hukumar NOA da lambar yabo

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, NOA, ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar Malam Lanre Issa Onilu, ta samu Lambar Yabo ta Kwarewa a Gyaran Ɗabi’u da Gina Ƙasa. Cibiyar Centre for Positive Value Reorientation and Advocacy ce ta bayar da lambar yabon a yayin ƙaddamar da littafinta “Paradise at a Crossroads,” a NBA Hall, Ilorin. An […]

Read more

Sojojin Najeriya sun kashe manyan mayaƙan ISWAP

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Haɗin Kai da ke aiki a yankin arewa maso gabshin Najeriya, sun sanar da nasarar kai wasu munanan hare-hare kan ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke addabar yankin. A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar, ya ce bayanan sirri sun tabbatar […]

Read more

Yan sanda sun harbe ’yan bindiga 4 a Binuwai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai, sun kashe wasu ’yan bindiga huɗu bayan sun kai hari wani shingen binciken ’yan sanda a garin Orokam da ke Ƙaramar Hukumar Ogbadigbo. Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ta ce lamarin ya faru ne ranar Laraba lokacin da jami’an Operation Zenda Joint Task Force ke aiki a shingen. Ta bayyana […]

Read more

ECOWAS ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Guinea

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta amince da ɗage dukkan sauran takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasar Guinea bayan kammala miƙa mulki, lamarin da ke nuna cikakken dawowar ƙasar cikin harkokin ƙungiyar yankin. An cimma wannan matsaya ne a yayin taron shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ECOWAS da aka gudanar a ƙasar […]

Read more