Sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’addar ISWAP 38 a jihar Borno.

Kakakin rundunar da take yaki da yan ta’adda a arewa maso gabashin najeriya Llaftanar Kanal Sani Uba ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a yau asabar.

Sanarwar tace yan ta’addar sun kai wani sansanin sojojin hari a yakin mandaragirau dake jihar Borno to amman sojojin suka bude musu wuta.

Kamar yadda ya bayyana sojojin tsanan ta wuta kan yan ta’addar wanda yasa suka sami kashe guda 38.

Sanarwar tace daga nan kuma sojojin sama suka kawo dauki inda suka bude musu wuta ta sama.

Ta kuma bayyana cewa sauran yan ta’addar sun zubar da makaman su inda tsere zuwa daji.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.