Dokta Hakeem Baba Ahmed Ya Ajjiye Mukamin Da Gwamnatin Tinubu Ta Bashi
Tsohon mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa.
Tsohon mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa.
Rahotanni daga karamar hukumar Okehi a jihar Kogi, mazabar Sanata Natasha Akpoti, na cewa Shugaban karamar Hukumar Amoka Monday, ya sanya dokar hana fita, saboda matsalar tsaro biyo bayan hana tarukan siyasa da na jama’a ba bisa ka’ida ba.
Sanata Natasha Akpoti wadda a kwanan nan Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar na tsawon watanni shida, ta ce “babu gudu babu ja da baya dangane da gangamin gaisuwar Sallah” da ta shirya yi a mazaɓarta.
Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan mutane 16 da aka yi a jihar Edo, yana mai umartar hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka yi wannan mummunar aika-aikar.
Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso,da tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗantakarar shugabcin ƙasar a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar sun yi tir da kisan ‘yan Arewa a jihar Edo, inda suka nemi a gudanar da bincike.
Gwamnatin Jihar Borno, ta ce ta ɗauki matakin hukunta Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri saboda mangwaro.
Majalisar Wakilan Najeriya ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas.
Rundunar sojin Isra’ila ta fara samame ta kasa a kudancin zirin Gaza lamarin da ya jawo martini daga kasashen duniya.
Tsohon gwamnan jihar kano kuma shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027 idan Allah ya kai mu.
Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da dokar ta baci, da kuma dakatarwar da shugaba Tinubu ya yi wa gwamanan jihar Ribas Siminalayi Fubara cikin yanayi na kusan na bai daya.