Wadan Da Suka Ci Zarafin Yarinya A Kan Mangwaro Basu Ci Bulus Ba— Zulum

Gwamnatin Jihar Borno, ta ce ta ɗauki matakin hukunta  Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri saboda mangwaro.

Bayan bayyanar wani faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin, lura da yadda mijin ya rika dukan yarinyar.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta musu sassauci ba.

Ya ce ma’aikatun shari’a, ilimi, da harkokin mata sun haɗa kai domin ganin an hukunta waɗanda suka aikata laifi.

Yarinyar, wacce ɗaliba ce, ta shiga harabar gidan ma’auratan domin tsinkar mangwaro bayan tashi daga makaranta, inda suka yi mata dukan kawo wuƙa.

A halin yanzu tana kwance a asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda Dokta Lawan Bukar Alhaji ya ɗauki nauyin jinyarta.

Gwamnatin Borno ta kuma tallafa wa iyayen yarinyar da kayan agaji, abinci, da kuɗi.

Iyayenta da sauran jama’a sun yaba wa gwamnatin kan matakin da ta ɗauka na kare haƙƙin yarinyar.

Gwamnati ta jaddada cewa duk wanda aka kama da cin zarafin yara ba zai tsira daga hukunci ba

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda