Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin A Kamo Makasan ‘Yan Arewa A Edo 

Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan mutane 16 da aka yi a jihar Edo, yana mai umartar hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka yi wannan mummunar aika-aikar.

“Ba za a bari miyagu su ci gaba da zubar da jinin ‘yan Nijeriya ba tare da hukunta su ba.

“Dole ne a yi adalci,” a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar.

Umurnin na shugaba Tinubu na zuwa ne a dai-dai lokacin da batun ke ƙara ɗaukar ɗumi a sassan Najeriya, musamman Arewacin ƙasar in da jama’ar da aka yi wa kisan gillar suka fito.

Post masu alaƙa

An dakatar da shugaban NSCDC a Neja kan mutuwar masu haƙar ma’adanai 37

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta raba wa iyalan jami’anta 62 sama da Naira miliyan 34

Gwamnati ta sa dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga a Neja