Majalisar Wakilai Ta Musanta Karɓar Kuɗi Kan Saka Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Majalisar Wakilan Najeriya ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas.
Majalisar Wakilan Najeriya ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas.
Rundunar sojin Isra’ila ta fara samame ta kasa a kudancin zirin Gaza lamarin da ya jawo martini daga kasashen duniya.
Tsohon gwamnan jihar kano kuma shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027 idan Allah ya kai mu.
Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da dokar ta baci, da kuma dakatarwar da shugaba Tinubu ya yi wa gwamanan jihar Ribas Siminalayi Fubara cikin yanayi na kusan na bai daya.
A ranar Talata ne, Shugaba Tinubu ya sanar da sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, inda ya bayyana cewa rikicin siyasar jihar yana barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya, inda mutane da dama ke ganin hakan bai dace da kundin tsarin mulki ba.
Ƙungiyoyin NLC da TUC sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta janye wannan mataki, don kada ya jefa Najeriya yanayin saɓa wa doka a nan gaba.
DAGA: Khaleepa Shareep Sharifai Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Similanayi Fubara daga muƙaminsa. Hakan na ƙunshe cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai cike da ƙorafi da majalisar ta fitar, inda take shirin tsige Gwamnan tare da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu. A cikin wasiƙar wadda take kafa hujja ta tanadin da Kundin […]
Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce zai yi magana da Vladimir Putin a ranar Talata don diga wa yakin Rasha aya.
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu shi ɗan APC ne, kuma ya fi so a rinƙa alaƙanta shi da jam’iyyar. Wannan dai ya biyo bayan wata tattaunawa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi da BBC ranar Alhamis inda ya ce “sai da Buhari ya amince sannan na bar […]
Daga : Shareep Khaleepha Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya bar jam’iyyar PDP. Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023 ya sake jaddada goyon bayansa ga hadakar jam’iyyun siyasa don kayar da jam’iyyar APC a 2027. Daily Trust ta rawaito cewa, a baya-bayan nan, rahotanni daban-daban […]
Rahotanni daga jihajihar Zamfara Arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu magoya bayan jam’iyyun adawa na AAC da PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.