Atiku Ya Bayyana Matsayarsa Kan Cigaba Da Zama A PDP

Atiku Abubakar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya

Daga : Shareep Khaleepha

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya bar jam’iyyar PDP.

Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023 ya sake jaddada goyon bayansa ga hadakar jam’iyyun siyasa don kayar da jam’iyyar APC a 2027.

Daily Trust ta rawaito cewa, a baya-bayan nan, rahotanni daban-daban sun nuna cewa Atiku yana tunanin barin PDP don shirin takarar shugaban kasa a 2027.

Rahotannin sun ce yana shirin komawa jam’iyyar SDP.

Amma a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar a ranar Asabar, an bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar na nan a matsayin cikakken mamba na PDP.

Post masu alaƙa

JIGAWA: ‘Yan siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.