‘Yan Jam’iyyar PDP Da AAC Sun Koma APC A Zamfara

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Rahotanni daga jihar Zamfara Arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu magoya bayan jam’iyyun adawa na AAC da PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Rahoton jaridar Leadership, ya bayyana cewa jam’iyyun na AAC da PDP sun samu koma baya sakamakon ficewar mambobin nasu zuwa APC.

Shugabancin APC na Zamfara ne ya karbi mutanen lokacin wani taron da aka gudanar a ranar asabar data gabata.

Cikin mutanen da suka canja shekar akwai dan takarar gwamnan Zamfara na jam’iyyar AAC a zaben shekarar 2023, Muhammad Kabir Sani, da tsohon dan takarar majalisar dokokin jihar na PDP.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Alhaji Isiyaka Ajiya Anka, shine ya karbi sauyin shekar mutanen.

Post masu alaƙa

Tinubu ya isa Kenya don halartar taron ƙoli na Afirka da Faransa

Gwamnati ta tilasta yi wa ɗaliban sakandare gwajin ƙwaya a Najeriya

SDP ta zaɓi Farfesa Sadiq Gombe a matsayin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa