Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sauya sunan Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Kano, zuwa Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule.
Marigayi Alhaji Maitama Sule, wanda ya rayu tsakanin shekarar 1929 zuwa 2017, ya ba da gudunmawa sosai ga ci gaban zamantakewa da siyasar Nijeriya a tsawon rayuwarsa.
Marigayin ya taba zama wakilin Najeriya na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, inda ya kasance shugaban kwamiti na musamman a Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da wariyar launin fata.
Ya kuma kasance dan majalisa kuma mai tsawatar a majalisar wakilan Najeriya tsakanin 1954 zuwa 1959.
Sannan shi ne kwamishina na farko a hukumar karbar korafe korafe ta Kasa a shekarar 1976,kafin daga bisani ya zama ministan ma’aikatar ma’adanai ta kasa.
- Mutum 1 Ya Rasu 21 Sun Jikkata Sanadiyar Fashewar Tukunyar Gas : Yan Sandan Kano
- An Ware Asibitoci 154 Domin Kulawa Da Mata Masu Ciki Kyauta A Najeriya
A Kano kuma ya rike mukamai da dama ciki harda kwamishinan yada Labarai.
A wata takarda da mai magana da yawun Shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar ya ce Shugaban Tinubu ya yi ammanar cewa sanya sunan Marigayin Maitama Sule a jami’ar ta gwamnatin tarayya dake Kano zai sa a ci gaba da tunawa dashi.
Haka kuma ya ce hakan zai zaburar da matasa masu tasowa su yi koyi da halayensa musamman tabbatar da gaskiya da kishin kasa da halaye na gari da aka san marigayi Dan masanin Kano da su tun yana raye.