Shugaba Bola Tinubu ya ba da damar ɗaukar sabbin jami’an tsaron daji 1,000 da kuma tura wata tawaga ta ceto mutane ta musamman biyo bayan sace malamai da ɗalibai da aka yi a jihar Oyo .
Mai magan ada yawum shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, shi ya bayanna wannan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi bayan wata ziyarar da wata tawagar gwamnatin tarayya ta kai ƙauyukan Esiele da Yawota a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo State bayan sace ɗalibai da malamai daga makaranti a yankin ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 2026.
“A wani ɓangare na matakan ƙarfafa tsaro a yankin, Shugaba Tinubu ya ba da damar ɗaukar jam’ian tsaron daji 1,000 a jihar Oyo a wani aiki na haɗin gwiwa da gwamnatin jihar,” in ji sanarwar.
“Tawagar ta kuma sanar da shugabannin al’ummomin da ‘yan majalisa cewa za ta miƙa buƙatarsu ta kafa sansanin soji a yankin ga shugaban ƙasar domin ya duba ya kuma amince da shi,” in ji shi.
Bugu da ƙari shugaban ya kuma ba da umarni ga wani birged na tsaro mai ƙarewa na musamman wajen ceto mutane ya ƙara matsa kaimi wajen tabbatar da an sako ɗaliban da malamansu.
Tawagar wadda ke ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu da babban sufeto janar na ‘yansanda , Tunji Disu da ministan tsaro, Christopher Musa da kuma babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan watsa labarai, Sunday Dare.
Tawagar ta bayyana matuƙar damuwar shugaba Tinubu game da lamarin da kuma yadda ya jajirce domin tabbatar da dawowar waɗanda aka sacen cikin aminci.
Mai bai wa shugaban shawara game da harkar tsaro, Nuhu Ribadu da sufeto janar na ‘yansan, Olatunji Disu da ministan tsaro, Christopher Musa da kuma shugaban ma’aikan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, sun kai ziyara Ogbomoso, da ke jihar Oyo , ne ranar Asabar domin ganawa da shugabanin al’ummomi da iyalai.