EFCC Ta Saki Tambuwal

Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shaki iskar ’yanci bayan sakinsa da Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta yi a yammacin wannan Talatar.

A jiya Litinin ce aka ruwaito cewa EFCC ta tsare Tambuwal a hedikwatarta da ke Abuja, inda take zargin ya fitar da wasu kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba har naira biliyan 189 a lokacin da yake rike da madafan iko.

 

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa