Gamnatin Jihar Kano Ta Janye Dokar Hana Zirga-zirgar Ababen Hawa

Gwamantin Jihar Kano ta sanar da janye dokar hana zirga-zirga da ta sanya a safiyar jiya Litinin bayan sanar da sakamakon zaben gwamna da na ’yan majalisar jihar.

Gwamnatin Kanon ta sanya dokar hana fita ne a jihar da nufin kauce wa tabarbarewar doka da oda biyo bayan bayyana sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na Kano, Muhammad Garba, shi ya sanar da dage dokar a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya.

Ya ce gwamnatin ta dage dokar  bayan ta yi nazari sosai kan lamarin da kuma kwanciyar hankali da ya wanzu a fadin jihar.

Kwamishinan ya yi kira ga bankunan kasuwanci da ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su fito su ci gaba da sana’o’insu na yau da kullum.

Post masu alaƙa

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.

Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta kaddamar da rumbum abinci ga jama’ar kudu maso kudancin Najeriya.