Gobara Ta Tashi a Kasuwar Onisha a Jihar Anambra

Gobara ta tashi a cikin wani gini da ake kira White House a baban kasuwar Onitsha dake jihar Anambra.

Gobarar ta tashi ne a sashen  dakin ajiyar  kaya na Gbongoro, wanda ya kasance waje ne a bayan kasuwar da ake sayar da tufafi kamar yadudduka da sauran kayayayakin sakawa.

Karanta Wannan: Gamnatin Jihar Kano Ta Janye Dokar Hana Zirga-zirgar Ababen Hawa

Mahukun dai suna nan suna nazarin musabbabin tashin  gobarar  da aka wayi gari da ita  a safiyar yau Talata.

Gobarar dai ta janyo asarar kayayaki na milliyoyin Naira.

‘Yan kasuwar na kokarin kashe  gobarar yayin da wasu kuma ke ci gaba da kiran jami’an kashe gobara.

Shedun gani da ido sun bayyana cewar gobarar ta tashi a gurin da ake siyar da kayayyakin dinki na White House, wanda a ƙa’ida wajen ajiyan motoci ne da fitar gaggawa amman ‘yan kasuwar suka toshe hanyar da shaguna na wucin gadi.

Post masu alaƙa

An yi garkuwa da ɗalibai a hanyar zuwa jarrabawar JAMB

Mai Ilimi na gaske ba ya Fariya ko dagawa – Sarki Aminu Ado Bayero

Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur karo na biyar a watan Maris