Gobe Za A Rufe Kasuwar Singa Domin Yashe Magudanan Ruwa

Hukumar kasuwar Singa da ke Kano ta ce gobe Lahadi 15 ga Yuni, 2025, ba za a gudanar da harkokin kasuwanci ba daga ƙarfe 7 na safe zuwa 7 domin aikin yashe magudanan ruwa.

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban Hukumar Gudanarwar Kasuwar Singa, Barr. Junaidu Muhammad Zakari, ya fitar.

Ya ce aikin na ranar Lahadi zai kasance aikin gayya na musamman da ya haɗa dukkanin masu ruwa da tsaki a kasuwar, tare da nufin tsaftace muhalli da inganta yanayin kasuwanci, musamman a lokacin damina ke kankama.

Shugaban hukumar ya buƙaci ’yan kasuwa da maziyartan kasuwar da su ba da haɗin kai tare da bin umarnin rufewar domin gudanar da aikin cikin tsari da kwanciyar hankali.

Post masu alaƙa

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu