Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alƙawarin taimakawa masana masu bincike akan ciwon ƙoda da ke addabar jama’ar wasu yankuna a jihar.
Kwamishinan lafiya a ji Jigawa, Honorabul Dokta Muhammad Abdullahi Kainuwa ne ya bayyana hakan a wani taron wayar da kai akan ciwon ƙoda a Haɗejia.
Kungiyar Likitoci ta Najeriya ne dai ta shirya taron a garin Haɗejia, ɗaya daga cikin yankunan da ke fama da samun mutane masu ciwon ƙoda.
- Yau Ake Bikin Ranar Birane Ta Duniya
- Alh. Muhammad Babandede Ya Zama Jagora A Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai Ta Ƙasa
Kainuwa ya bayyana cewa zai yi amfani da damarsa, wurin haɗa masu niyyar yin bincike mai zurfi akan ciwon ƙoda da waɗanda za su ɗauki nauyin binciken.
Ya ce zurfafa bincike akan ciwon ƙoda zai taimaka wurin magance ciwon cikin gaggawa.