Gwamna Umar A. Namadi, ya amince da naɗin Farfesa Muhammad Ibrahim Yakasai, a may sabon shugaban jami’ar Sule Lamiɗo, Kafin Hausa (SLU)
Wannan amincewa na ƙunshe ne a cikin jawabin da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim, ya fitar.
Sannan ya yi ƙarin haske da cewa naɗin nasa ya biyo bayan miƙo sunansa da Majalisar Gudanarwar Jami’ar ta yi kamar yadda yake a kunshe cikin kundin kafa wannan jami’a.
Kafin naɗa shi a wannan muƙami, Farfesa Muhammad Ibrahim Yakasai, shi ne shugaban kwamitin tabbatar da Ingancin ayyuka na jami’ar Bayero.
Sannan ya taɓa zama shugaban sashen kara sani na ilimin jami’a, wato Post Graduate Studies.
An haifi sabon shugaban jam’iyyar ne a garin Garin Gabas ta ƙaramar hukumar MalamUmar Namadi Madori a 1960.
Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Bayero, inda ya karanci Fannin Koyarwa da Tarihi a 1986. Sai kuma ya yi digirinsa na biyu a fannin Ilimin Adamtaka a 1991 tare da yin digiri na uku a dai fannin Ilimin Adamtaka daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.