Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi Ya rage lokacin aikin ga ma’aikata Saboda azumi

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a lokacin azumin watan Ramadan.

‎Gidan Rediyon Jihar Jigawa ya rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Shugaban Ma’aikatan Jihar, Muhammad K Dagaceri, ya sanyawa hannu a ranar Laraba 18 ga Fabrairu 2026.

‎Sanarwar ta ce bisa sabon tsarin, ma’aikata za su rika zuwa aiki daga karfe tara na safe zuwa karfe uku na rana a ranakun Litinin zuwa Alhamis, maimakon karfe biyar na yamma.

‎A ranar Juma’a kuma, za su rika zuwa aiki daga karfe tara na safe zuwa karfe ɗaya na rana.

‎Muhammad K Dagaceri ya ce an hakan ne domin saukaka wa ma’aikata Musulmi tare da ba su damar samun isasshen lokaci domin gudanar da ibadu da sauran ayyukan alheri a cikin watan mai alfarma.

‎A ƙarshe, sanarwar ta bukaci ma’aikata su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da bunkasar tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.

Post masu alaƙa

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC

DSS ta kama mutane 5 da ake zargi da sace ɗaliban makarantar St. Mary’s Pipiri a jihar Neja