Jami’an ICPC sun bincika gidan El-Rufai da ke Abuja

Jami’an Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC sun binciki gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Abuja a ranar Alhamis.

Mai bai wa tsohon gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

A cewarsa, j”ami’an hukumar sun isa gidan El-Rufai inda nan take suka fara binciken dukkan sassan gidan.

Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya yi Allah wadai da matakin, yana mai cewa “binciken da jami’an suka yi ba bisa ƙa’ida ba ne kuma ya saba wa dokoki da haƙƙoƙin ɗan Adam.”

Tun a ranar Laraba hukumar ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana hannunta dangane da wani bincike da take yi.

Hukumar ba ta bayar da cikakken bayani kan irin binciken da ake yi a kansa ba.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda