Nentawe Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban APC

Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da nadin Farfesa Nentawe Yilwalda daga jihar Filato a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

An cimma matsayar ne yayin taron kwamitin zartarwar na kasa da ya gudana a Abuja.

Taron wanda ke gudana a fadar shugaban ƙasar, ya samu halartar Shugaba Bola Tinubu da kuma gwamnonin jam’iyyar ta APC

Wane ne Farfesa Nentawe Yilwalda?

Kafin zaɓensa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na riƙon ƙwarya, Farfesa Nentawe Yilwatda ya kasance ministan jin-ƙai na Najeriya.

Sunan Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ɓulla a baya-bayan a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda ake kyautata zaton za su maye gurbin Ganduje.

Tsohon malamin jami’ar ya fito ne daga jihar Filato, kuma ya koyar ne a Jami’ar ayyukan noma da ke Makurdi kafin tsunduma cikin harkokin siyasa.

Haka nan ya taɓa zama kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya tsakanin shekarun 2017 da 2021 a jihohin Benue da Anambra da Osun da Rivers da kuma Cross River.

Masu lura da al’amura na ganin sabon shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya, Farfesa Nentawe Yilwalda ka iya zama cikakken shugaban jam’iyyar ko da bayan babban taronta na watan Disamba.

A watan Disamba ne jam’iyyar mai mulki za ta yi babban taronta na ƙasa domin zaɓen shugaban jam’iyyar mai cikakken iko.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda