Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayyana damuwarsa game da watsi da gine-ginen ofisoshin da aka fara ginawa a hukumar ta Hizba da ke Sharaɗa.
Wannan na zuwa ne a lokacin da gwamnan ya kai ziyarar aiki hukumar domin ganin irin yadda shirin auren gata da aka fi sani da auren zaurawa ke tafiya.
Ana sa ran yin auren gatan ne a ranar 13 ga watan da muke ciki, inda ake sa ran aurar da mutane dubu ɗaya da ɗari takwas daga ƙananan hukumomi 44 da huɗu dake faɗin.
A yayin da yake bayyana dalilin kawo ziyara hukumar, gwamnan Kano, ya ce, ya je hukumar ne domin ganin irin halin da hukumar ke ciki da kuma yadda gwamnatinsa za ta inganta ayyuka da ofisoshi da samar musu da kayan aikin da suke buƙata wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Sannan gwamanna ya nuna gamsuwarsa da irin yadda aka shirya gudanar da shirin auren gata tare da yaba wa hukumar ta Hizba da Ma’aikatar Lafiya ta jihar nan.
Shi ma, shugaban hukumar ta Hizba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya jinjina wa gwamnan bisa ƙoƙarin cika wa al’ummar jihar alƙawarin da ya ɗauka na auren gata a lokacin yaƙin neman zaɓensa.
Ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda ya dawo ya samu hukumar bayan shekaru takwas da barin hukumar ba tare da wasu sabbin ayyuka na daban ba a hukumar.