Gwamnatin jihar Kano ta karyata rade-radin shirin rushe sababbin masarautu

Gwamnatin jihar Kano ta karyata rade-radin da ake cewa ta dauki mataki akan sababbin masarautu.

Sakataren yada labarai na  gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin-Tofa shine ya bayyana hakan, inda ya ce, har yanzu babu wani mataki da gwamnati ta dauka akansu.

Sunusi Bature ya ce, ba za su boye duk wani abu ba tsakanin bangaren gwamnati da majalisa ba domin bawa al’ummar jihar Kano damar sanin abinda yake faruwa akan matakan da gwamnati take dauka.

Da safiyar ranar Talata ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nemi sahallewar majalisar na daukar mutum 20 a matsayin masu bashi shawara, kuma tuni majisar ta amince a zaman da tayi na farko.

Ana saran a sati mai zuwa gwamnan jihar Kano zai tura sunayen kwamishinoni zuwa majalisa domin tantancewa.

Post masu alaƙa

Jirgin sojin Najeriya ɗauke da mutum 32 ya faɗi a Ondo

Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?

Matasan Arewa sun bukaci gwamnonin arewa maso gabas su fi bai wa tsaro da samar da aikin yi muhimmanci