• Home  
  • NDLEA Ta Kama Iyali Guda Bisa Zargin afarar Kwayoyi
- Babban Labari - Labarai

NDLEA Ta Kama Iyali Guda Bisa Zargin afarar Kwayoyi

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta kama wani ɗankasuwa da matarsa da ‘ya’yansa mata biyu da zargin safarar ƙwaya. National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) ta ce ta kama mutumin mai suna Ajah Johnson Uchenna ne bayan gudanar da bincike da kuma wasun ayyuka kafin hakan. Zama A APC Babban […]

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta kama wani ɗankasuwa da matarsa da ‘ya’yansa mata biyu da zargin safarar ƙwaya.

National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) ta ce ta kama mutumin mai suna Ajah Johnson Uchenna ne bayan gudanar da bincike da kuma wasun ayyuka kafin hakan.

Kakakin NDLEA Femi Babafemi ya faɗa cikin wata sanarwa cewa ‘yansandan farin kaya ne suka fara kama mutanen tun ranar 13 ga watan Yuni, amma da bincike ya tsananta sai aka sake kai samame gidansu ranar 1 ga watan Yuli a jihar Legas.

An kama su ne da ƙunshin ƙwayar skunk mai nauyin 277.5kg tun da farko, kafin a sake gano wata mai nauyin 231kg, inda daga nan ne aka mayar da su hannun NDLEA.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai