Ministan yaɗa labaran Najeriya Mohammed Idris ya gargaɗi ƴan ƙasar kan amfani da ƙirƙirarrun bidiyo domin nuna shugabannin ƙasar a wani yanayi mara kyau domin ɓata musu suna.
Jaridar The Nation mai zaman kanta ta ruwaito ministan yana cewa, “mun ga yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira ta hanyoyin da suka dace, da hanyoyin da ba su dace ba. Zai iya yiwuwa kana zaune a nan kawai sai wani ya yanko kanka ya ɗaura a wani jikin domin ɓata maka suna.”
- Gwamnatin Gombe Zata Gina Mayankar Dabbobi Kan Biliyan 3
- Salah Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Premier Na Bana
“Muna ganin yadda ake juya maganar shugaban ƙasa, inda zai faɗa abu daban, amma sai a canja abin da ya faɗa. Ko kuma minista ya faɗa wani abu, sai a juya masa magana,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa suna duba lamarin sosai a matakin gwamnati, “musamman yadda za mu tsaftace kafofin sadarwa ba tare da tauye haƙƙin furta albarkacin baki ba.”