Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Peter Obi ya zargi Gwamnatin Tarayya da ƙulla maƙarƙashiyar hana shi yin takara a zaɓen shekarar 2027.
Haka kuma Obi ya ƙalubalanci dukkan masu neman takarar shugaban ƙasa, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, da su fito muhawarar bainar jama’a kan tsare-tsaren da suke da shi ga ƙasar.
“Ina ƙalubalantar duk wani mai takara da ya fito mu yi muhawara don ya faɗi abin da yake son yi wa wannan ƙasa, ciki har da Shugaba Bola Tinubu. Ba don na faranta muku rai nake faɗin hakan ba, a’a, don a canza Najeriya kuma a gyara ta,” in ji shi.
Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra ya shaida wa ɗaliban cewa ba burin kansa ba ne yake yi, a’a, don muradin ganin ƙasar ta gyaru ne.
Haka kuma Obi ya yi tsokaci game da hukuncin Babbar Kotun Tarayya wadda ta soke wani hukunci na baya da ke umartar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta yi rajistar Jam’iyyar NDC a matsayin jam’iyyar siyasa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wata Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta soke hukuncinta na baya wanda ya umarci INEC da ta yi rajistar NDC a matsayin jam’iyyar siyasa